Siyasa

An kai Hari Akan Tawagar Dan Takarar Gwamnan Ondo a PDP, Jegede yace Yunkurin Kashe shi akayi.

Spread the love

Eyitayo Jegede, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Jihar Ondo da za’ayi ranar 10 ga Oktoba, 2020, ya bayyana harin da aka kaiwa tawagarsa a ranar Laraba a matsayin “yunƙkurin kisan kai”.

Jegede ya zanta da manema labarai a ofishin kamfen dinsa da ke Akure jim kadan bayan da wasu ‘yan daba dauke da makamai suka far wa ayarin motocinsa a garin Oba Akoko.

Ya ce shi da magoya bayansa sun ziyarci fadar Oloba na Oba Akoko don ziyarar kafin yakin neman zabensu lokacin da ’yan bangan siyasar APC, da ke dauke da makamai suka fara kai musu hari.

Mun ji karar harbe-harbe a wajen fadar Oloba na Oba Akoko wanda ke kusa da babbar hanyar.

“An yi ta harbe-harbe a kan ayarin mu da ke kusa da fadar daga tarin‘ yan daba da ke cikin motocin yakin neman zaben APC tare da Gwamna Rotimi Akeredolu da ke jagorantar ayarinsu Inji Shi.

“A yayin harin, motoci 15 a cikin ayarin mu sun lalace yayin da mutane da dama kuma suka jikkata yayin harin Inji Shi.”

Ya bayyana cewa ya yanke shawarar dakatar da yakin neman zaben sa ne da zai gudanar a Ayegunle da ke Oba Akoko saboda harin kuma don gudun zubar da jini.

Jegede ya ce ‘Yan Jam’iyarsa ta PDP sunje garin, Oba Akoko bayan jam’iyyar ta samu amincewar kwamishinan ‘yan sanda don gudanar da kamfen dinsu.

Dan takarar na PDP ya kara da cewa, an kai rahoton harin da aka kai wa ayarin motocin nasa ga Kwamishinan ’Yan sanda na jihar da kuma Daraktan Ma’aikatar Harkokin Jiha.

Ya kara da cewa, “Wannan a bayyane ya ke game da kokarin kashe rayuwar dan Adam. Ba mu taba yarda da cewa za mu zo cikin wannan mawuyacin hali a jihar Ondo ba kuma ni da kaina ban ga irin wannan bakin cikin a rayuwata ba.

“Idan wani abu ya same ni ko wani daga cikin mutanenmu a wannan jihar, ina kira ga jama’a da su san wanda za su dora wa alhakin hakan.

“Amma kuma, za mu kare kanmu, ya zama dole mu kare kanmu a wannan mummunan aikin.”

Don haka, ya yi kira ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda da ya hanzarta yin bincike game da harin da aka kai wa ayarin motocinsa tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button