Labarai
An kama jarumar film tsirara tare da dan cikinta..
An Kama Wata Jarumar Film Saboda Ta Saki Hotonta Tsirara.
An Kama ‘Yar wasan Ghana, Akuapem Poloo saboda hotonta na tsiraici tare da ɗanta dan shekara bakwai.
Wannan kame ya zo ne kwanaki Kadan bayan da kungiyar kare hakkin yara ta nemi Sufeto-janar na ‘yan sanda a kasar ta Ghana ya bincikita game da batun rigimar da danta yayi ranar haihuwarsa, wanda ya yi a yanar gizo.
A hoton, wanda ta sanya a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, jarumar ta Dora Hoton da rubutu domin murnar ranar haihuwarsa .
Ta ce ta yanke hukuncin tsirara ne a gaban ɗanta wanda ke cikin rigarta kawai saboda ta haife shi tsirara.