An Kama Kananan Yara Masu Shekaru 18,16 Da 15 Da Suka Yi Garkuwa Da Wani Yaro A Bauchi.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Hukumar ‘yansandan jihar Bauchi ta kama wani matashi dan shekaru 18 wanda dalibine a kwalejin ilimi ta AD Rufai, Muhammad Isa da zargin garkuwa da wani dan makwabcinsu.
An gabatar dashi ga ‘yan jarida tare da wasu masu laifi da dama inda ya amsa laifinsa. Sun sace dan makwabcinsu ne tare da wasu abokanshi 2 inda suka nemi a basu kudin fansa Miliyan 2.6.
Isa yace shi telane kuma har ma yana da shagon Dinki amma matsalar Annobar Coronavirus jarinsa ya lalace kuma ya tambayi mahaifinsa amma yace masa bashi da kudi.
Ya bayyana cewa wani abokinsa ne Abdulgafar Adamu shima dan shekaru 18 ya bashi shawarar yin wannan avu kuma bai yi wata-wata ba ya amince.
Yace daga baya yaso ya janye amma bai san abinda zai gayawa mahaifansa ba. Akwai dayan wanda suka yi satar tare Ahmed Usman dan shekaru 15 dake ajin sakandire.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mr. Lawal Tanko Jimeta yace nan bada dadewa ba za’a gurfanar da wanda ake zargi a kotu.