Tsaro

An kama masu Garkuwa da mutane su Takwas a kan Iyakar Najeriya da Kamaru.

Spread the love

Dubun wasu matasa Su Takwas masu garkuwa da Mutane da Fashi da makami, ya cika a kan Iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Kamaru.

Wannan Nasarar na zuwa ne bayan Makonni biyu da Aka cimma matsaya kan tsakanin Jami’an Tsaron Najeriya da na Kamaru kan Yakar Yan Fashi da makami da masu garkuwa da Mutane da suka Addabi Yankin.

Matasan An kamasu ne da Gaggan Makamai a Wajensu.

Wadanda aka kame sun hada da Umaru Shehu, Isyaku Dauda, ​​Hammadu Yusuf, Beto Yusuf, Mohammed Abubakar, Mohammed Jao, Adamu Jaunga da Mohammed Ali.

Shugaban karamar hukumar Maiha ta jihar Adamawa, Dakta Idi Aminu, ya tabbatar wa wakilinmu cewa an kama mutane takwas a kusa da kan iyaka da Kamaru.

Ya ce, Da farko an kama daya daga cikinsu wanda hakan ya sa aka kama wasu wadanda dukkansu suka amsa laifinsu da aikata laifin satar mutane da dama a jihar.

Matasan sun fito ne daga karamar Hukumar Song kuma sanannu ne.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button