Tsaro
An Kama Uwa Da Ya’yan’ta Da Suka Kware Wajen Garkuwa Da Mutane A Kano.
Da yake yin jawabi, kwamishinan ‘yan sandan jihar kano CP Habu A Sani a hedkwatar rundunar ‘yan sandan jihar kano dake bomfai a karamar hukumar Nassarawa.
Habu A Sani yace Jami’an ‘yan sandan sunyi nasarar kama ‘yan fashi kimanin guda 30 da kuma masu garkuwa da mutane su 25 a fadin jihar, Ciki har da uwa da ‘ya’yanta wadanda suka kware wajen yin Garkuwa da Mutane.
A Karshe ya ce za bayan sun kammala binccike zasu gurfanar da masu laifin agaban kotu domin su gurbi abin da suka shuka.
Daga Kabiru Ado Muhd