Labarai
An karawa Alkalin Daya Kori Shari’ar Atiku Akan Shugaba Buhari Mukami.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Mai shari’a Muhammad Garba da yayi watsi da karar da dan takarar shugaban kasa a 2019 karkashin PDP, Atiku Abubakar ya shigar kan kalubalantar zaben shugaban kasa,
Muhammadu Buhari na cikin wanda majalisar Alkalai ta kasa, NJC ta bada sunansu a kara masa mukami zuwa kotun kolin Najeriya.
Shine Alkalin da ya jagoranci shari’ar Atiku a shekarar 2019 a kotun daukaka kara wanda kuma yayi watsi da korafin na Atiku.
Sannan kuma ya fitone daga yankin Arewa maso yamma.Kaman yanda muka Kawomu cewa NJC a zaman da ta yi na ranekun 11 da 12 ga watan Augusta ta mikawa shugaba Buhari shawarar Alkalan da ya kamata a baiwa mukaman wanda mai Shari’a garba ba ciki.