Labarai
An Kashe Dan Sandan Dake Tsaron Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero Agaban Matarsa Da Dansa.
Daga Kabiru Ado Muhd
Wasu ‘yan bindiga daba’asan ko suwaye ba sun kashe Dan Sandan dake gadin Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero kisan gilla a birnin Kano.
Lamarin ya faru ne a jiya litinin da tsakar dare, a unguwar kureken Sani dake karamar hukumar kumbotso a jihar Kano.
Wata ‘Yar uwar mamacin ta shaidawa shugaban rundunar ‘yan sandan Kano cewa maharan dauke da miyagun makamai sun afkawa gidan Jami’in Dan sandan cikin dare inda sukayi masa kisan gilla a gaban matar Sa da Dan Sa.
Dan sandan da aka hallaka shine babban me tsaron lafiyar sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado bayero a duk inda yake.