Uncategorized

An Kashe Fasinjoji 10 Tare Sace Wasu Da Yawa A Wani Hari A Borno.

Spread the love

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe akalla mutane 10 tare da yin awon gaba da wasu fasinjojin da ba a bayyana adadin su ba a karamar hukumar Kaga da ke jihar ta Borno, in ji majiyoyi.

Wadanda lamarin ya rutsa da su galibin fasinjojin da motocinsu suka tsaya a kan hanya biyo bayan takaita zirga-zirgar ababen hawa da yamma.

Lamarin ya faru ne da karfe 7 na dare a kauyen Wassaram, da ke Ngamdu Ward na karamar Hukumar Kaga a daren Talata.

Wata majiya ta ce mutane da yawa kuma sun jikkata kuma maharan sun sace fasinjoji da yawa.

Majiyar tsaron wacce ba ta so a ambaci sunanta ba, ta ce wadanda abin ya rutsa da su a cikin motocin kasuwanci biyar sun yi tsaye a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu biyo bayan hana zirga-zirgar ababen hawa da sojoji sukayi.

“Boko Haram sun zo Wassaram ne da misalin karfe 19:30 na daren ranar Talata.

“Mun gama sallar dare kenan. “Sun kai kimanin 30 kuma sun zo ne a cikin motoci uku na musamman.

“Sun hadu da wasu mutane yayin da suke shiga kauyen. “Sun fadawa mazauna cewa su kaura daga wurin domin wasu mutane na zuwa su kawo musu hari.

“Don haka, mutane suka fara gudu ba su sani ba mutanen da ke cikin motocin uku‘ yan Boko Haram ne.

“Sun fara bude musu wuta. “Sun kashe mutane 10, wasu da yawa kuma sun ji munanan raunuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button