Tsaro

An kashe mutane shida, 20 sun Bace a Nasarawa.

Spread the love

Kimanin mutane shida ne wasu ‘yan bindiga da ake zargin Fulani makiyaya ne suka kashe a, Daisy Umaisha Development Area na jihar Nasarawa.

An rawaito cewa sama da gidaje 12 ne ‘yan bindigar suka tayar da su yayin harin.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa, an kwashe dabbobinsu da kayan abinci da yawa a yayin artabun.

Ya ce, ‘yan bindigan sun afka wa al’ummomin kan babura sama da 30, daga nan suka fara harbin mutane ba baji Ba gani, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida.

Majiyar ta kara da cewa har yanzu ba a gano kimanin mazauna kauye 20 ba sakamakon mamayar.

Allah ya Kawo mana Karshen wannan Masifar.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button