Labarai

An Kone masallaci a Billiri Rikincin na kokarin rikidewa zuwa na addini.

Spread the love

Rikicin Sarauta a tsakanin kabilar Tangale daje garin Billiri jihar Gomhe ya fara juyewa zuwa rikicin addini

Kwanakin baya Sarkin Tangale wanda ba Musulmi ba ya mutu, yanzu kuma wanda Gwamnatin jihar Gombe ta zaba ya maye gurbinsa Musulmi ne kasancewar ya gaji Sarautar, sai wadanda ba Musulmi ba suka ki amincewa duk da kabilarsu daya

Rikicin nasu na Sarauta yana neman sauya salo zuwa rikicin addini, domin har an kona Masallaci a garin Billiri a yau

Menene laifin Masallaci akan rikicin Sarauta da za’a konashi?
Hakika wadanda suka kona Masallacin ba su nemi zaman lafiya ba, ya kamata hukuma ta zakulosu don su fuskanci hukunci

Muna fatan Allah Ya kawo zaman lafiya a garin Billiri daga datti datti

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button