An kore shi daga Makarantar NDA domin yaki aminta ya aikata muggan laifuka
Cigaba Da Binciken dalilin korar Sojojin a Makarantar koyon aikin Soja ta NDA
Da muka gabatar da bincikenmu kan tabbacin dalilin dayasa makarantar ta NDA ta Kori matashi M.I Daura bayan kammala karatunsa sai muka samu cewa akwai son zuciya da Rashin adalci aciki domin ita makarantar dalilin da ta bayar sune na cewa anga fuskar M.I Daura A gidan TV acewasu ana Masa Interview)
Wato yadda sashin dokar tsarin makarantar yake shine sau daya 1 ake Binciken salsalar baya (Dossier Review) Kuma idan baka samu nasarar tsallake Binciken na salsalar baya ba to bazaka samu damar fita passing out) daga makarantar ba
bayan M.I Daura ya tsallake duk wani sharadi ya Samu damar fita daga makarantar ta NDA sai ya cigaba da zuwa Nnc onne domin ya riga ya gama da NDA
amma wani abin mamaki sai suka sake dawo dashi da zummar kamashi da laifi Kan cewa iyayensa sun shirya masa walima Kuma Acikin walimar ta godiya ga allah Yayi magana da NTA Yana Mai cewa Ina mai Godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya bani dama na samu nasarar kammala karatuna na fita daga NDA. Sai suka dauki wannan suke amfani da shi a matsayin laifi a gare shi Wanda Kuma a dokar makarantar basu da Ikon dawo dashi bayan ya fita Yayi Passing out.
amma wannan duk bashi ne abin dubawa ba Kuma Bai Isa laifin da za’ayi Masa haka ba duk wannan matsala ta samo asali ne domin kawai shi Lt conel YM dodo Yana da matsala dashi Yana so ya saka Matashin dabi’ar nan ta’aikata miyagun laifuka Wanda zamuyi bayaninsu Nan gaba idan ana bukatar Hakan amma matashin M.I Daura Din Yaki aminta, Haka Kuma Bincikenmu ya tabbatar mana wannan shi ne asalin matsalar da tasa aka dawo da M.I Daura Bayan Ya Fita daga Makarantar ya gama komai na aikin horon soja ya zauna a Makarantar ba tare dayin komai ba domin ya riga da ya gama Horonsa..
Har’ila yau kawai sai wata Rana da sanyin safiya suka zo Suka Fara gudanar da aikin sake duba salsalar baya Dossier Review) a watan Janairu Zuwa watan Satumba na 2019 da Janairu 2020 domin kawai suna neman karamin laifi don anfani dashi su Kori M.I Daura amma ba’a same shi da wani laifi ba sun hana shi zuwa hutun Kirsimeti domin suna nemansa da sharri
da Suka nemi laifin M.I Daura Suka Rasa Shine Sai suka kawo ra’ayin sake duba salsalar baya a watan Janairu wanda Hakan ya sabawa kundin tsarin littafin su na 2018 domin sau daya akeyi a shekara shine sai suka kawo jerin sunayen 54 kadets wa’yanda Suka ce sun kora shi Kuma M.I Daura sukace sun sami tauwaya guda goma 10 Entries) Cikin Binciken salsalarsa Dossier Review) wanda kuma hakan ba Gaskiya bane
Domin shi M.I Daura a lokacinma bashi a Kasar a Disamba na 2018 zuwa Janairu 2019 da kansu Suka bashi izinin zuwa Saudiyya don yin ibadar Allah.
Kafin su kore shi sun kulleshi na tsawon kwana shida 6 suna gana Masa azaba sun kwace wayarsa daga karshe wani Ofisa Mai suna MAJOR EJOUFOR ya bashi umarnin dole Kan ya jefar da wayar tasa ya fasa ta yayi Hakan ne domin goge duk wata sheda da’ike Acikin wayar akwai shedu manya manya da shi M I yake dasu. Koda wani Kwamanda a wajen yace kar ‘a fasa wayar sai shi EJOUFOR Yace wannan umarni ne aka bashi daga ADJUTANT ACADEMY wato LT COL DODO.
Yanzu Haka an zabi wasu an dawo dasu wa’yanda suke dauke da matakin laifuka ashirin 20 acikin binciken salsalarsu Dossier Review) fiye da matakin Kaso 70% nai laifin na Wanda Suke da mataki Manjo Biyar 5 ma’ana gwari gwari dole sai ka Kai matakin Manjo hudu 4 kafin Makarantar ta iya korarka Amma dukda sharance sharance da akayima shi M.I Daura mataki uku da rabi 3+ kawai aka samu akansa Wanda Hakan ya nuna Basu da damar korarsa a Makarantar…
Kenan Batun ya tabbata laifin sa shine kin aminta da aikata laifin kin aminta da aikata muggan laifuka luwadi yasa aka kore shi, abin takaici ne ace sojan daya samu horon YAQE YAQE kala kala shine za’ayima irin wannan korar ta wulakanci Don kawai yaki aminta da bukatar wani, to kenan yaushe za’a kawo karshen ta’addanci a Nageriya?
Zamu cigaba bibiya tare da bincike Kan Al’amari…