Kasuwanci

An Rufe Shahararriyar Kasuwar Siyar Da Wayar Salula Ta Farm Center Dake Kano A Yau.

Spread the love

Jami’an kotu bisa rakiyar Jami’an tsaro sun rufe kasuwar farm center ta jihar kano.

Bayan da ‘yan kasuwar ta farm center suka isa kasuwar sai suka tarar da jami’an kotu sun lika wata takarda dake dauke alamar cewa an rufe kasuwar sakamakon kasuwar ta zama mallakin wani mutum daya mai suna Alhaji Muntari.

Alhaji Muntari wani mutum ne da ya dade ana rigima dashi a kotu akan cewa gaba daya filin kasuwar ta farm center mallakin sa ne.

An tambayi ‘yan kasuwar ta farm center game da wannan hukunci da suka wayi gari dashi, sai sukace su ba a sanar dasu hakan ba, ba a basu wani notice ba, su dai sunzo sun tarar an aiwatar da hukuncin ne kawai, amma suna kira ga gwamnatin kano da ta shigo cikin lamarin.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button