Labarai
An sace basarake tare da mutun 15 a jihar Katsina
‘Yan Bindiga Sun Sace Basaraken Gargajiya da Wasu mutun 15 A Kauyen Katsina
Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun sace basarake a daren ranar Litinin tare da wasu mutane 15 da ke karamar hukumar Danmusa a cikin jihar Katsina.
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan bindigar da yawansu ya kai mamaya kauyen da tsakar daren Litinin kuma suka yi aiki na tsawon sa’o’i bayan haka suka tafi tare da wadanda lamarin ya rutsa da su.