Tsaro

An Sace Jami’in DSS, An Nemi N100m A Matsayin Kudin Fansa.

Spread the love

Awanni kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’in DSS, Sadiq Bindawa a Katsina, an sake garkuwa da wani jami’in a Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun sace jami’in ne tare da dansa mai shekaru hudu a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a Kaduna.

Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan jami’in da ba a bayyana sunansa ba sun nemi a biya N100m kudin fansarsa.

‘Yan bindiga sun sace jami’in hukumar ‘yan sandan farin kaya, DSS, tare da dansa mai shekaru hudu a ranar Asabar a jihar Kaduna.

Jami’in da a yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Rahotanni sun ce yan bindigan sun tuntubi iyalansa sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 100 kafin su sako shi.

Jami’in da aka yi garkuwa da shi yana aiki ne a matsayin mai kula da inda ake ajiye makamai na makarantar horas da sabbin jami’an DSS.

Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan yan bindiga sun kashe wani jami’in DSS mai shekaru 33 mai suna Sadiq Abdullahi Bindawa duk da kudin fansa Naira miliyan 5 da aka biya.

Marigayi Bindawa yana gidansa ne da ke bayan sakatariyar gwamnatin tarayya a Katsina yayin da yan bindigan suka kai masa hari. Bindawa yana aiki ne da sashin tattara bayannan sirri na hukumar da ke Abuja.

Marigayi Bindawa yana gidansa ne da ke bayan sakatariyar gwamnatin tarayya a Katsina yayin da yan bindigan suka kai masa hari. Bindawa yana aiki ne da sashin tattara bayannan sirri na hukumar da ke Abuja.

Daga Amir sufi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button