Tsaro

An sace Matafiya Mota guda a Hanyar Sokoto zuwa Katsina.

Spread the love

Mun samu rahoton sace mutane mota guda da suka taso daga sokoto zuwa katsina.

Lamarin ya farune da wata mota cikin motocin Sokoto Transport, abin ya faru ne a Dai dai kauyen Kwashabawa dake karamar hukumar zurmi ta jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne Yau alhamis da misalin karfe 10 na Safe.

Jihohin Sokoto, Zamfara da katsina dai daman sunyi kaurin suna wajen matsalar Tsaro da Ta addabi Arewa maso yammacin Kasar Nan.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button