Tsaro
An Sace ‘Yan Mata da Mata a Zabarmari Inda Aka Yanka Manoma~ Majalisar Dinkin Duniya.
Mai kula da ayyukan Jinkai Na majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon yace “an sace mata da ‘yan Mata a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari kan manoma suka kashe manoma 110.
Kallon yace “lokacin da Na ziyarci zabarmari domin jajantawa ‘yan garin Na kadu matuka yadda Na tausayawa al’ummar garin, mazauna garin sunce akwai Mata da ‘yan mata da ba’a gansu Ba, kuma Tun daga Ranar Asabar da aka kai harin Har zuwa yau Mutane Na kara mutuwa a asibitocin da ake kula dasu.
Sannan yace akwai bukatar a hada karfi da karfe domin kawo karshen ta’addanci a Yankin.
Ahmed T. Adam Bagas