Labarai

An sake maka Ganduje a Babbar Kotun Nageriya kan sai ya sauka A Matsayin Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa.

Spread the love

Jigon jam’iya Kuma Tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa Mohammed Saidu Etsu ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Abuja domin neman ta soke nadin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

A cikin wani kwafin kudurin da Etsu ya gabatar a ranar Juma’a wanda muka samu, ya yi zargin cewa an nada Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa ba bisa ka’ida ba bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Wasu daga cikin bukatun da Etsu ya nema a gaban kotun sun hada da: “Odar ta soke nadin Dr Abdullahi Umar Ganduje da wanda ake kara na 3 ya yi a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa a ranar 3 ga watan Agusta 2023 bisa hujjar cewa wanda ake kara na 3 ya gaza, ya ki amincewa. ko kuma a yi watsi da tsarin da doka ta 31.5 ta Kundin Tsarin Mulkin APC (supra) ta shimfida.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button