An Sake Tsawaita Dokar Hana Tarukan Jama’a A Ghana.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Shugaban Ghana ya sanar da tsawaita dokar hana tarukan jama’a da suka hada da na gudanar da ibada da tarukan siyasa, har zuwa ranar 31 ga watan Mayu.
A jawabin da ya yi wa al’ummar kasarsa dangane da halin da ake ciki kan batun cutar corona, shugaban kasar Ghana Akufo-Addo ya ce; ya zuwa yanzu an yi wa mutane 160, 500 gwajin cutar corona a kasar, kuma an tabbatar da mutane 4,700 suna dauke da ita, yayin da 494 suka warke 22 kuma suka rasu.
A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa, shugaban na Ghana ya k ra da cewar karin wuraren da dokar hana tarukan ta shafa sun hada da, gidajen rawa, gidajen abinci da shaye-shaye, da kuma bukukuwa.
Haka nan kuma batun dokar hana tarukan jana’iza za a ci gaba da aiwatar da ita, matukar dai mutanen da za su halarta janazar ba su wuce 25 ba.
Shugaban na Ghana ya kirayi jama’a da su kiyaye ka’idoji da jami’in kiwon lafiya suke sakawa domin kaucewa kamuwa da cutar, tare da yin kira da a ci gaba da bayar da hadin kai ga jami’an na kiwon lafiya.