Tsaro
An Sako Sarkin Sarakunan Fulani Usman Adamu Wanda Aka Sace.
An sako Alhaji Usman Adamu, Sarkin Sarakunan Fulani wato Arɗon Arɗoɗi na Jihar Kwara, wanda wasu ‘yan bindiga suka sace a safiyar Alhamis da ta gabata.
An yi garkuwa da sarkin ne a kan hanyarsa ta shiga garin Ilori, babban birnin jihar.
A daren jiya ne aka sako basaraken a dajin Makwa na Jihar Neja a kan hanyar zuwa garin Kainji ba tare da an bayar da kuɗin fansa ba.
A yanzu Alhaji Usman Adamu yana asibiti, inda ake yi masa magani sakamakon duka da aka yi masa,sai dai babu rauni ko karaya a jikin nasa.
Sace sarkin sarakunan na Fulani makiyaya ya ƙara fito da irin yadda sace-sacen jama’a ke ci gaba da yin ƙamari a arewacin Najeriya kuma babu wanda ya tsira daga wannan matsalar.
Daga Amir Sufi