Labarai

An Sami Nasarar Kama Wasu Sojojin Bogi Bayan Sun Ladawa Wata Tsohuwa Dukan Tsiya.

Spread the love

An kama wasu da ake zargin sojojin bogi ne a kasuwar Ogun.

An kama wasu sojoji biyu da ake zargin na jabu ne a ranar 22 ga Satumbar, 2020 a yankin Sagamu na jihar Ogun.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Oyeyemi ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan kiran gaggawa da jami’in ‘yan sanda shiyya ta Sakura ya samu cewa mutane hudu da ke sanye da kakin sojan gona ba zato ba tsammani suka sauka daga motar Bas a Kasuwar Sabo, Sagamu, kuma sun haifar da rikicia can, inda suka yi wa wata tsohuwa’ yar kasuwa duka, da kuma dagula ayyukan kasuwanci.

Yayin da wannan ke gudana, wani sojan gaske ya isa wurin kuma ya nemi a ba su labarin wadanda ake zargin.

Da ike sun san kansu, sai suka fara hawa babura don tserewa daga wurin, saboda haka kiran ya aika da gaggawa ga ‘yan sanda.

Dangane da bayanin, DPO, Sakura Division, CSP Dahunsi Ronald, ya hanzarta jagorantar tawagarsa zuwa wurin, inda aka kama biyu daga cikin wadanda ake zargin tare da taimakon jama’a.

Jama’ar da suka fusata sun sun hau kansu, suka yi kokarin far wa wadanda ake zargin, amma da sauri ‘yan sanda suka batar da su daga wurin.

Wadanda ake zargin sune: Joseph Uzor, 27, da Obadeyi Quadr, 27. Abubuwan da aka samo daga gare su sun hada da: kayan sojoji biyu, kakin mayafi guda biyu, bakaken takalmi guda biyu, falmaran kamfuna daya, fes din camouflage daya, wayar Samsung daya da kuma kudi N10,800.

Oyeyemi ya ce ana zargin Uzor da Quadr da cewa suna daga cikin ‘yan kungiyar fashin wadanda suka saba aiki a kayan sojoji a kan babbar hanyar Shagamu zuwa Benin, wasu daga cikin kuma an kama su kwanan nan.

Kwamishanan rundunar, Edward Awolowo Ajogun, ya ba da umarnin a tura wadanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba zuwa sashen binciken manyan laifuka da binciken sirri na jihar.

Ajogun ya kuma ba da umarnin a gudanar da bincike a kan abubuwan da suka aikata a baya kafin a gurfanar da su a gaban kotun da ke da hurumin iko.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button