Labarai

An Samu Kwamishina Na Bogi Da Yaci Albashin Shekaru 2 A Jihar Neja.

Spread the love

Gwamnatin jihar neja ta fidda sanarwar Samun kwamishinan Gona na bogi da yaci albashin shekaru 2 a Jihar.

A ranar larabar da ta gabatane gwamnatin Jihar neja ta kori ma’aikata guda 80 da suka karawa kansu albashi ba bisa ka’ida ba, Shugabar Ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Hajiya Salamatu Abubakar CE ta sanarda korar ma’aikatan bayan majalisar zartaswar jihar ta amince da hakan.

Ma’aikatan da aka kora sun fito ne daga ma’aikatu daban daban na jihar kama daga Sashin ma’aikatar Shara’a, Ilimi, kiwon lafiya, makarantar fasahar kiwon lafiya, makarantar Unguwar zoma.

Bayan kwamishinan bogi da yaci albashin shekaru 2, akwai ma’aikacin Shara’a da ya ke karbar albashin babban Jojin Shari’ar Jihar, Akwai Wanda ya sanya sunan dan uwansa a wata ma’aikata ya karbi albashi har tsawon shekaru 11 Inji sanarwar.

A watan yuni ne aka kafa wani kwamiti da zai zakulo masu laifi a albashin gwamnatin Jihar, gwamnatin tace ta gano ma’aikatan bogin sun karbi Naira miliyan 672 a matsayin albashi na bogi.

Kwamishinan gona na yanzu na jihar Hon. Haruna Dukku, yayi Allah wadai da ma’aikacin da yaci albashi na mukamin Kwamishinan gona na bogi har tsawon shekaru 2.

Dukku yace wannan rashin Imani ne kaci albashin haramun irin wannan.

Idan baku manta ba a cikin makon da ya gabata gwamnatin jihar ta bankado Malaman framare marasa Karatu da na bogi har guda sama da 2880 a Jihar.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button