Tsaro

Harin Tawagar Zulum: Shugabannin Dattawan Najeriya Sun Tuhumi Dattawan Borno.

Spread the love

Majalisar Dattawan kishin kasa (PEC) ta tuhumi ‘yan uwanta dattawa daga arewa maso gabas da su jagoranci kiran ‘yan ta’addan Boko Haram da su mika wuya.

A wata sanarwa dauke da sa hannun Sakatare-janar din ta, Cif Simon Shango kuma aka gabatar da ita ga manema labarai a ranar Litinin, PEC ta kalubalanci shugabanni da masu ruwa da tsaki daga yankin da su tashi tsaye su yaki ‘yan ta’addan.

Kiran PEC din ya biyo bayan harin baya-bayan nan da aka kai wa ayarin motocin Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.

A cewar kungiyar, wasu shugabanni a yankin arewa maso gabas da kuma dangin al’ummomin da sake tayar da kayar baya sun kasa cika kokarin da Sojojin Najeriya ke yi na yaki da Boko Haram.

Sanarwar ta ce, hada karfi da karfe tsakanin Sojoji a yakin da kuma masarautun gargajiya da ‘yan siyasa na da matukar mahimmanci wajen kawo karshen yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button