Siyasa

An Tashi Baran Baran Tsakanin Trump Da Yan Jaridu.

Daga Haidar H Hasheem Kano

An tashi baran-baran tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da kuma ‘yan jarida, a taron manema labarai da ya gudanar jiya a fadar white house.

Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, a taron manema labarai da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gudanar jiya a fadar white house, shugaban ya yi kalamai na batunci da izgili ga wasu daga cikin manema labarai a wurin.

A lokacin da ‘yar rahoton tashar CBS Weijia Jiang ta tambaye kan kalaman da yake furtawa na cewa Amurka ce kan gaba a duniya wajen yaki da cutar corona, cewa idan haka ne me yasa kuma cutar tafi kamawa tare da kashe mutanen Amurka fiye da kowa a duniya.

Donald Trump ya amsa tambayar a cikin fushi, inda ya ce; wannan tambaya ce da ya kamata ki yi wa gwam,natin kasar China, ba ni ba.

Daga lokacin kuma Trumpya shiga yi ma ‘yar jaridar izgili da batunci, tare da kiransu a matsayin wadanda ba su san abin da suke yi ba, ya kuma ki amsa sauran tambayoyinta, kamar yadda ya ki ya amsa tambayoyin ‘yar rahoton CNN, daga karshe kuma ya juya cikin fushi ya tafi abinsa, a lokacin da ‘yan jarida suke gabatar masa da tambayoyi.

Wannan dai shi ne taron manema labarai na farko da Trump ya gudanar, tun daga ranar 27 ga watan Afiruln da ya gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button