Al'adu

An Tono Gawa Tana Numfashi bayan Ta Shekara guda da Mutuwa a Jihar Imo.

Spread the love

Abin Al’ajabi da ban mamaki ya faru a jihar Imo, inda aka ga gawa tana numfashi, Kamar yadda wani faifan bidiyon ya bayyana, gawar da ta shekara 1 a kwance aka gani tana numfashi, An ga yadda kwari suka fara cin akwatin gawar, amma jikin mamacin bai ru6e ba.

Wannan al’amari ya farune, a Umuoji, Amucha da ke jihar Imo, inda aka ga wani mutum da ya Mutu shekarar da ta gabata yana numfashi.

Jaridar The Nation ta wallafa, bidiyon a shafinta Na Facebook, inda ta nuna mutane sun taru a kan akwatin gawar, inda aka ga mutumin yana numfashi. Mutanen sun yi ta ihu suna cewa “yana numfashi, yana numfashi” cike da mamaki. Kamar yadda labarin yazo, mutumin ya mutu ne ranar 9 ga watan Nuwamba, 2019 kuma an rufeshi ranar 8 ga watan Oktoban 2020, kamar yadda aka ji wani yana fadi a bidiyon.

An ji muryar wani mutum yana cewa, “mutumin nan ya mutu a shekarar da ta gabata da sati 3 kenan da birne shi, sai ga shi yana numfashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button