Rahotanni

An tura Matashi Gidan yari Kan post din cin Zarafin Gwamna Badaru a Facebook.

Spread the love

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Dutse, babban birnin jihar Jigawa ta yanke wa Sabi’u Ibrahim Chamo Zaman gidan yari saboda bata sunan gwamna Muhammad Badaru Abubakar.

An fara kama Mista Chamo ne a jajibirin Kirsimeti kuma aka tsare shi kafin a gurfanar da shi a gaban kotu saboda rashin tabbatar da zargin da ya yi a Facebook.
Laifin dayasa aka yankewa hukuncin ya yi zargin cewa gwamnan ya yaudari ‘yan takarar da yawa daga APC ta hanyar karbar kudinsu don ba su tikitin jam’iyyar.

A yayin shari’ar, bayan an karanta masa bayanan farko, Mista Chamo ya amsa laifinsa kuma kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida, tare da zabin biyan tarar N20,000 da kuma bulala 20 na sandar don zama abin hanawa ga wasu.

A watan Yunin 2017, an kama wani mai sukar gwamnan, Zakari Kafin Hausa kuma an tsare shi na tsawon kwanaki saboda sukar da gwamnan ya yi a shafukan sada zumunta. Rahotan Daily Nigerian.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button