Tsaro
An Yi Garkuwa Da Matar Aure Da Kanwarta A Kaduna..
Daga Abdul Aziz Muhammad
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wata matar aure da kanwarta a unguwar Sabon Gero da ke Sabon birnin Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Litinin, wanda hakan ya jefa akasarin mazauna unguwar cikin tashin hankali.