Mata iyayenmuUncategorized

Anyiwa yarinya yar wata uku a duniya mafi munin fyade

Spread the love

Daga Datti Assalafy

Wannann itace Rukayya jaririya ‘Yar wata uku tare da mahaifiyarta Maimuna, wani tsinanne marar imani yabi dare ya dauketa ya mata fyade a lokacin suna bacci, da ya gama lalata yarinyar sai ya dawo da ita ya ajiye ya gudu, wannan mummunan aika-aika ya faru ne a garin Adogi dake jihar Nasarawa

A yanzu haka suna babban asibitin koyarwa na garin Jos jihar Pilato, wanda yayi mata fyaden ya dagargaza farjin jaririyar, Likitoci sunyi mata aiki na farko, da na biyu da na uku, saura aiki na hudu, raunin da kuke gani a kan cikinta Likitoci ne sukayi domin kokarin gyara farjin yarinyar saboda ba zata iya yin bawali da fitsari ta farjinta ba sakamakon fyaden da aka mata

Kamar yadda nace jaririyar da Mahaifiyarta Maimuna yanzu haka suna asibitin koyarwa na Jos, Maimuna tace babu abun da suke bukata sai taimakon ‘yan-uwa Musulmai don basu da abincin da zasuci balle kudin asibiti ya kare, gashi za’a sake yin aiki na hudu nan da kwana kadan

Muna kira ga ‘yan uwa Musulmai na garin Jos don Allah kuje asibiti ku taimaki wadannan bayin Allah, sannan jama’a ku taimaka da sharing saboda a gani a kai musu tallafi, mai neman karin bayani zai iya kiran wadannan nambobin waya 08030614481/09036327619

Muna rokon Allah Ya bawa jaririyar lafiya, wanda yayi mata fyaden muna rokon Allah da SunayenSa Tsarkaka ya tsine masa albarka, ya tona masa asiri, Allah Ya hadashi da dukkan bala’i da masifa a ko’ina yake Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button