Ana Samun Karuwar Tsadar Kayan Abinci A Najeriya.
Farashin Abinci na dada karuwa a jahohin kudu dakuma arewacin Najeriya.
D farko dai gari, wani kalar Kayan Abinci ne da mafi akasari yarbawa dakuma sauran kabilun Najeriya ke amfani dashi, kuma Kayan Abinci ne dake da saukin kudin gaske.
Sai dai a wannan lokaci Garin yayi Tsadar da ba’ayi tunanin zaiyi a wannan shekarar ba.
Wata Yar kasuwa daga Jahar Enugu dake kudancin Najeriya ta tabbatarda cewa a baya Suna sayarda litar 4.5 ta gari akan kudi Naira 350,amma a yanzu Suna sayardashi akan kudi Naira 650, wanda hakan ke nuna Saura Kadan Garin ya ninka kudinsa.
Ta shaidawa hakan ya faru ne sanadiyar tsadar doya a kasuwanni.
Sannan Kayan Abinci Kama daga Gero, shinkafa, dawa dakuma dawa farashinsu na Kara tashi.
Mafi akasari akan samu tashin farashin Kayan Abinci a lokacin damina, dakuma saukarsa a lokacin girbi.
Daga Abdullahi Muhammad Maiyama