Labarai

Ana Zargin Jaruma Nafisa Abdullahi Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Da Safara ‘Yan Mata Zuwa kasashen waje.

Spread the love

Wani mai rajin kare hakkin bil’adama, mazaunin garin Abuja, Lawal Muhammad Gusau ya zargi jarumar Finafinan Hausa Nafisa Abdullahi, da Fataucin miyagun kwayoyi da kuma safarar yara.

A wata takardar korafi da Gusau ya fitar a ranar Juma’a 25 ga watan Disamba 2020, ya bayyana jarumar a matsayin wadda ta kware wurin fataucin kwayoyi da kuma fasa kwaurin yara.

Gusau ya ce, Nafisa tana da kamfani mai suna Nafs Entertainment One Dream wanda aka yi mata rijista da shi a matsayin kamfanin nishadantarwa, amma sai ta ke amfani da shi don shigar da yara marassa gata wurin sanyasu a cikin Finafinai, amma a bisa binciken da su ka yi.

Abubuwan da ake zargin jarumar tana fataucin su sun hada: Benylin, Codeine, Pantazocine, da Tramadol.

Haka zalika a cikin takardar korafin Gusau ya ce Nafisa tana fakewa da tafiye-tafiye zuwa kasashen turai, tana tunkaho da ita ‘yar fim ce. Amma maganar gaskiya ita ba cikakkiyar Bahaushiya ba ce, Kabilar Birom ce, wanda sanannen yare ne a jihar Plateau.

A cewar sa wani abin takaicin shi ne, ta yi watsi al’adun mu ta koma kwaikwayon al’adun yammacin kasashe.

A karshe ya nemi jama’a da su yi bincike mai zurfi don gano ayyukan jarumar da kuma na kamfanin ta.

Gusau ya rubuta wannan korafi ne, baayan jarumar ta saki wasu zafafan hotuna a shafukanta na sada zumunta, a yayin ziyararar ta kasashen ketare.

A lokacin da kafar watsa labarai ta Kannywood Exclusive su ka tuntubi jarumar game da zargin da ake mata, sai ta ce:

“Me zan ce? Me kuwa zan ce? Daman akwai mutane marasa aikin yi haka a duniya?

To, ai basu ma san me suke yi ba! ni ina da Kamfani one dream ne?
Kamata ya yi, idan za su yi rubutu irin wannan, su samu bayanai na daidai mana.

Ta ci gaba cewa mahaifina cikakken dan Kano ne, mahaifiyata ce yar Jos kuma ba birom bace.”

Daga Kannywood Exclusive

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button