Fashion

Ana Zargin Jarumi Lawan Ahmad da sace milyan goma…

Spread the love

Umar shine sabon mai kula da asusun ajiyar masana’antar (Company Accounter) Malam umar ya kasance mai tsoron allah cikin aikinsa tare da aiki bisa gaskiya, da zuwansa ya fara kawo tsari mai kyau ga masana’antar komai ya fara tafiya bisa tsari….

Sai dai kash wata budurwa matashiya itace ke Jagorantar masana’antar bayan mahaifinta ya dora ta matsayin shugaba..

Tana da kyau…

Tana da girman kai…

Tana da son izza…

bata son raini…

tana matukar son a girmama ta, bataso ace tayi Kuskure…

Malam Umar Sabon Accounter Shi kuma Bazai iya hakan ba…
Ta rantse da allah sai ta wulakanta shi…

Ta biya kudi mai tarin yawa ga matar banza domin samun Bidiyon tsiraicinsa da ita matar banzar amma Umar ya tsallake…

To Yanzu kuma sai gashi ta kama shi da zargin satar kudin masana’anta (Company) Har Naira milyan goma 10millions kuma bisa alama malam umar bashi da wata hujjar cewa bashi bane ya sace kudin…

Sarkakiya ce mai tarin yawa da Lawan Ahmad ya shiga amatsayin umar Accounter na Company amma fa wannan duk acikin Film mai suna Izzar so…

Me kake tunanin zai iya faruwa? domin kallon yadda zata kaya ku kasance da tashar Bakori TV dake kan YouTube wanda suke kawo wannan shirin film na Izzar so mai dogon zango a duk ranar Lahadi da misalin karfe takwas 08:00pm

ko kuma ku shiga wannan alqaluma (links) kai tsaye zuwa ga tashar ta BakoriTV👇🏽

Idan Kun shiga saikuyi Subscribe Sa’an nan ku danna kararrawar sanarwa ta yadda za’a samu damar sanar daku idan an dora sabon shiri a tashar ta BakoriTV

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button