Labarai

Anfanin Rayuwarka shine hidimtawa bil’adama ~Rahma Sadau Ga Buhari.

Spread the love

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta bayyana kashe-kashen da ‘yan ta’adda ke yi a arewacin Najeriya a matsayin“ Rashin hankali ”.

Jarumar, wacce ta bayyana hakan a wasu sakonninta na Twitter a ranar Talata, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da duk hukumomin da abin ya shafa da su tashi tsaye wajen daukar nauyin kare rayuka da dukiyoyi a kasar.

Rahma_sadau ta rubuta cewa, “Rashin tsaro da muke (fuskantar) a halin yanzu a arewacin Najeriya ba a magance shi ba kuma ya kamata a magance shi ba tare da bata lokaci ba.

Ma’anar rayuwa ita ce yiwa bil’adama hidima, to amma ta yaya zamu bautawa rayuwa alhali mun rasa tunanin mutumtaka?

“Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su amsa su kuma kare mu daga karuwar yawan cin zarafin mata da kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.”

Sadau ta jawo cece-kuce a watan da ya gabata saboda sanya hotonta a kan kafafen sada zumunta sanye da rigar mara baya da rashin rufe gashin kanta wanda hakan ya saba wa dokokin addinin Musulunci.

Daga baya masana’antar fina-finai ta arewa ta dakatar da Sadau yayin da yawancin mabiya addinin Islama da ke arewacin kasar suka yi mata suka kuma sukayi barazanar kai mata hari.
Daga baya jarumar ta goge hoton kuma ta nemi gafarar masoyanta amma da yawa sun zarge ta saboda jawo maganganu marasa kyau game da addinin Islama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button