Labarai
Anga Dorinar Ruwa A Kauyan Kebbi Bayan Ambaliyar Ruwa..
Kwanaki kaɗan bayan ambaliyar ruwan da akayi a jahar Kebbi, kwatsam sai jama’ar ƙauyan zaria kala-kala dake jahar suka fara hangan dorinar ruwa na kiwo a bakin kogin.
Awani rubuta da uwargidan gwamnan jiha Kebbi Dakta Zainab Bagudu ta walafa a shafinta na Twitter, ta ce anga Dorinar Ruwan ne a ƙauyan Zaria kala-kala.
Ta bayyana cewa a makon da ya gabata ne ambaliyar ruwa ta lalata mana gonakinmu, irin abubuwan dake faruwa hakan yana ƙara tabbatar mana da cewa batun sauyin yanayi gaskiyane a wanan ƙarnin.
Daga Amir Sufi📝