Annobar tsintsaye ta Sauka a faransa
Jama’ar Faransa da ke daya daga cikin kasashen Turai da Corona ta tagayyara sun firgita sakamakon samun bullar murar tsuntsaye a gari na biyu a kasar.
Ma’aikatar Noma da Kiwo ta rawaito sanarwar da Ofishin Tsare Lafiyar Jama’a ya fitar inda aka fadi cewar an kashe dubunnan daruruwan kaji sakamakon kamuwa da murar tsuntsaye a garin Yvelines baya ga Tsibirin Korsika.
Sanarwar ta ce, kwararru na gudanar da binciken gano alakar bullar cutar a garuruwan biyu daban.
A gefe guda kuma, gwamnati ta fara daukar matakan hana cutar kama wasu dabbobin na daban.
A farkon watan Nuwamba ne Faransa ta killace dabbobin da ake kiwo a gida sakamakon yadda tsuntsaye masu gudun hijira suka sauya hanyarsu tare da bi ta cikin kasar Faransa.
A kasuwannin kasar kuma an hana sayar da tsuntsayen gida da na daji, LABARAI 24