Ansa dokar Hana Fita a Jihar adamawa
Gwamnan jihar Adamawa Hon. Ahamadu Umaru Fintiri ya sanya dokar hana yawo a jihar na tsawon sati biyu. Dokar zata fara aiki ne daga daren Jumma’a 24 ga watan Afrilu zuwa ranan jumma’a 8 ga watan Mayu 2020.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata takaddan manema labaru da mai magana da yawun gwamnan Solomon Kumangar ya rattaba hannu a kai.
Takaddan tace daukan wannan mataki ya zama tilas ga gwamnatin jihar saboda kiyaye lafiya da rayukan jama’a a jihar.
Saidai takaddan ta bayyana cewa dokar bata shafi wasu kebantattu ba kamar ‘yan jarida, masu sayar da abinci, jami’an tsaro, masu aiki a ma’aikatan bada ruwa, yayinda bankuna kuma zasu gudanar da takaitattaccen ayyuka.
Kazalika takaddan tace za’a kafa kotun tafi da gidan ka don hukunta masu karya doka nan take.
Jihar Adamawa dai ta shiga sahun jihohi da suke da masu dauke da cutar Covid-19 a ranar laraba da ta gabata.
Wanann shine karo na biyu da gwamna Ahmadu Fintiri yake kafa dokar hana fita a jihar na makonni biyu.