Labarai

Anyi Kira ga Buhari Lallai yayi murabus ko Kuma a tsige shi.

Spread the love

Adeyanju, hadimin kungiyar ‘Concerned Nigerian Group’, ya ce yawan sace-sacen mutane da ake yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya isa dalilin da zai sa shugaban kasa ya yi murabus ko kuma a tsige shi.

Ya yi kiran ne yayin da yake zargin cewa ana sace sama da mutane 100 ta wannan hanyar a wasu a Lokaci daya.

A cikin sakon Twitter, Adeyanju ya rubuta: “Adadin mutanen da aka sace a kan hanyar Kaduna kadai ya isa sanya shugaban kasa yin murabus ko a tsige shi.

Majiyoyi da yawa sun ce wani lokacin ana sace mutane sama da 100 a wannan hanyar kuma ba ‘ a cika bayarda da rahoton matsalolin ba. ”

Tsawon lokaci, yawaitar rashin tsaro a Arewa ya zama abin firgici, musamman sace-sacen mutane da ‘yan fashi.

A ranar 17 ga Nuwamba, 2020, an sace daliban jami’ar Ahmadu Bello, ABU, Zariya tara kuma aka nemi kudin fansa na N270m.

Wannan ya dalilin yasa Datti Garba, dan majalisar wakilai ya gabatar da kudirin sanya katanga jami’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button