Siyasa

Anyi Kira Ga Hajiya Fatima Abacha (Gumsu) Data Fito Takarar Sanata A Kano Ta Tsakiya.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Wata kungiyar matasan jihar kano da sukayi taro a sakatariyar Audu bako dake nan kano sunce Hajiya Fatima Abacha ce ta can-canci wakiltar Kano ta tsakiya a zaben 2023 mai zuwa duba da yadda mata suke da tausayi.

Shugaban matasan Comrade Zubairi ya ce yanzu lokaci ya yi da zasu farka daga bacci susan inda suka dosa a siyasance, don haka wannan karan kuma mace zasu gwada a Kano ta tsakiya.

Yakara da cewa Fatima Abacha tana da kwarewa, suna sa ran za tayi abin da yawancin mazan da suka wakilci Kano ta tsakiya basuyi ba, domin Fatima Abacha tana da tausayi, gata da son ganin rayuwar talaka ta inganta.

Shugaban kungiyar yace kira sukeyi ga Hajiya Fatima Abacha data amsa wannan kira nasu, kuma suna fatan zataji wannan kira nasu a matsayinsu na matasa.

Taron dai ya samu halartar shugabannin kana nan hukumomi 15 na Kano ta tsakiya, wanda ya gudana a sakatariyar Audu bako dake nan kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button