Labarai

Anyiwa Yar Shekara Goma Sha Biyu Fyade, Kuma Ta Samu Juna Biyu A Jahar Sokoto.

Spread the love

Matar Gwamnan Jahar Sokoto Hajiya Maryam Mairo Aminu Waziri Tambuwal ta gana da wata yarinyar shekaru Sha biyu da akayiwa fyade kuma ta haifi yaro a Jahar Sokoto.

Lamarin ya faru ne a garin Wajeke dake karamar Hukumar wamako a Jahar Sokoto.

Andai kori uwar Yarinya da yarinyar daga garinsu na wajeke sanadiyar wannan lamari.

Matar Gwamnan Jahar Sokoto ta bada umurnin Gudanarda bincike tare da samawa mahaifiyar Yarinya dakuma yarinyar gida a cikin garin sokoto.

Takuma samarwa yarinyar unguzoma da zata kula da ita.

Bayan wani lokaci yarinyar ta haifu kuma an radawa yaro suna fodio.

Sai dai da take ganawa da yarinyar, matar Gwamnan Jahar Sokoto Maryam Mairo ta baiwa yarinyar shaarwarinta suka dace, tare da tunatarda ita cewa taji tsoron Allah.

Matar Gwamnan ta bayyana cewar yanzu haka akwai yara da dama da suke daukar nauyinsu ta hanyar gyara musu illar da suka samu yayin fyaden.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button