Siyasa

APC Ta Maka INEC Da NNPP Kotu Akan Sakamakon Zaben Gwamnan Kano

Spread the love

“Bayanan wanda ya lashe zaben kamar yadda INEC ta sanar ya sabawa dokokin da suka tsara yadda za a gudanar da zaben baki daya.”

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta umurci kungiyar lauyoyin ta da ta nemi hakkinta kan ayyana dan takarar gwamna kuma zababben gwamnan jihar New Nigeria People Party (NNPP) Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kakakin jam’iyyar, Ahmed Aruwa ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya yi ikirarin cewa sanarwar ta sabawa dokokin zabe da aka shimfida.

Ya ce, “Jam’iyyar APC ta Kano ta caccaki sakamakon da INEC ta bayyana, wanda ya tabbatar da dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

“Bayyana wanda ya lashe zaben kamar yadda INEC ta sanar ya saba wa tanadin dokokin da suka tsara yadda za a gudanar da zaben baki daya.”

Duk da cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Nasiru Gawuna ya taya zababben gwamnan murna, jam’iyyar na neman a yi masa shari’a.

Mista Aruwa ya yi zargin cewa “INEC ta yi sabanin tanade-tanaden dokokin zabe inda ta ayyana Abba Gida Gida a matsayin zababben gwamnan jihar”.

Dangane da halin da ake ciki, shugabannin jam’iyyar na jihar sun umarci hukumar ta ta da ta ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar da ke zamanta a filin kotun Miller Road.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button