Arewa Media Writers Ta Jinjinawa Gwamna El-rufa’i, Saboda Rushe Gidan Da Aka Shirya Yin Sharholiya.
Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, tana jinjinawa gwamnan jihar kaduna Nasir E-lrufa’i, kan namijin kokarin da yayi wajen hana yin sharholiya tsirara, tare da rushe gidan da aka shirya yin sharholiyar a ciki.
Idan baku manta ba cikin wannan makon wasu batagarin matasa suka shirya taron fasikanci na murnar sabuwar shekara, tsakanin maza da mata inda suka sanya sharuda ga mahalartan sharholiyar, wajibi ne ga duk wanda zai halarci sharholiyar dole yazo tsirara haihuwar uwarshi da kororon roba tare da sanarwar cewar sun ajiye ‘yan mata guda 50 domin a yi fasinkanci dasu a yayin sharholiyar, bayan kowa ya biya kudin shiga mai mataki-mataki daga kan 10,000 zuwa matakin 5,000 da 2,000.
Gomna Nasir El-rufa’i, ya nuna bacin ransa da takaicin sa akan batagarin matasan da suka yi kokarin shirya wannan sharholiyar, ya kama dukkannin matasan da suka shirya wannan fasikancin, tare da rushe gidan da aka shirya yin sharholiyar.
Kungiyar “Arewa Media Writers” tayi matukar farin ciki da wannan babban aikin da Gwamnan yayi, inda kungiyar ta ayyana Gwamna Nasir El-rufa’i a matsayin jajirtaccen shugaba dake kishin al’ummar yankin Arewa, wannan babban abin farin ciki ne garemu da duk wani dan Arewa mai kishin yankin.
Kungiyar “Arewa Media Writers” tana yiwa Gwamna Nasir El-rufa’i, addu’ar fatan alkhairi tare da goya mishi baya kan wannan aiki da yayi na ganin ya samar da tsabtatacciyar tarbiya ga dukkannin al’ummar yankin mu na Arewa.
Haka zalika kungiyar “Arewa Media Writers” a shirye take da ta bada gudummuwarta ga dukkannin wani abu da za’a aiwatar don kawo wa al’ummar yankinmu na Arewa cigaba mai dorewa.
Fatan Kungiyar “Arewa Media Writers” shine Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a yankinmu na Arewa dama kasar Nijeriya baki daya. Amin.
Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”