Kunne Ya Girmi Kaka

Asalin Hausawa.

Spread the love

Hausa harshe ne na Hausawa, su kuwa Hausawa wata al’umma ce da suke zaune a ƙasar Hausa a cikin yankin Afrika ta yamma. Kuma su Hausawa mutane ne baƙaƙe, wato baƙar fata ba fara ba, ko da yake akan sami auratayya da wasu ƙabilu. Hausawa mutane ne masau riƙon al’adunsu na gar-gajiya, musamman wajen tufafi da abinci, da al’amuran da suka shafi aure da haiwuwa da mutuwa, da sauran sha’anin mu’amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni, da kuma al’amuran sana’a da kasuwanci da neman ilimi da sauransu.

Kamar yadda tarihi yanuna mafi yawan mazauna farfajiyar Afrika ta yamma mutane ne da ba su da karatu da rubutunasu na kansu, haka ma al,umar Hausawa, don haka zaiyi matukar wuya asani wani mai bincike kai tsaye da zaibigi kirji ya fadi tabbataccen lokacin da aka sami al’umar Hausawa, ko kuma asalinsu. Saboda rashin samun rubutaccen wan abu game dasu ya taimaka wajen bacewar tarihin nasu, domin kuwa samun rubutu da karatu a kasar Hausa bai dade sosai ba.

Masana da dama bakinsu ya sassaba wajen tabbatar da tarihin samuwar ilimin rubutu da karatu ga Hausawa. Alal misali, an ambaci cewa a wajajen 1349-1385 wasu malamai wangarawa kamarsu arba’in suka fara zuwa kasar Hausa don karfafa Addinin Musulunci, sun zo Kano da Katsina tare da litattafan koyarwa, kana suka kafa makarantu da masallatai, sannan suka sare wata bishiya da ake bautawa a Madabo birnin Kano, kuma wannan zuwa nasu shi ne mataki na farko na shigowar hanyar koyon karatu da rubutu a kasar Hausa ta hanyar Muhammadiyya.

Shi kuwa karatu da rubutu ta hanyar boko, ya samu ga Hausawa ne a farkon karni na ashirin, saboda a daidai shekarar 1900 ne gwamnatin Ingila ta karbe ragamar mulki daga hannun Sarakunan Hausawa. Amma a shekarar 1903 ne sojojin Gwamna Lugga suka cinye Kano da Sakkwato, kuma sai a cikin shekarar 1905 aka bude makaranta ta farko a Sakkwato don koyar da karatun boko tare da wasu malamai guda biyu, Mr. Burden da mataimakinsa Malam Ibrahim. Amma ita wannan makatranta bata dade ba, saboda iyaye sunki bayar da ‘ya’yansu don tsoron kada su koma kirista, don haka sai aka rufe ta.

Saiadai kuma a cikin shekarar 1909 sai Gwamna Lugga ya umarci wani Bature mai suna Mr. Hans Vischer (Dan Hausa), don ya sake bude wasu makarantun a lardi-lardi a fadin Arewa. To wannan shine farkon lokacin zuwan karatu da rubutu Kasar Hausa.

Saboda haka idan aka yi la’akari da abubuwan da suka gabata, zai bayyana karara cewa samun ilimi na karatu da rubutu ga Hausawa bai dade sosai ba, kuma hakan ya yi sanadin kasa samun kwakkwarar hujja game da tarihin Hausawa. Saboda duk wani abu da za a fada kodai kunne ya girmi kaka ne, ko kuma wani hasashe ne na masu bincike da basu da tabbas.

Amma abin lura anan shine abin da masana tarihi suka tabbatar a kai ya hada da asalin kalmar Hausa, da asalin Hausawa daga ina suke? Kana kuma da cewa yaushe aka fara amfani da ita kanta Hausar? Amma ko kadan kuskure ne a danganta rayuwar mutane da a gurbin da ake kira kasar hausa a yanzu, da kuma sarautunsu.

A kokarin da ake yi kan tabbatar da hakikanin asalin Hausawa da harshensu kuwa, masana da dama sun tofa lbarkacin bakinsu kamar dai yadda za a gani.

Alal misali wasu masana tarihi sun ambaci cewa akwai akwai mutane tun lokaci mai tsawo da ya shude a a wadannan garuruwa na kasar Hausa, kuma babu wanda zai bugi kirji ya ambaci daga ina suke. Ko da yake dai wasu sun ambaci ana kyautata zaton asalin Hausawa Barbarar-yanyawa ne tsakanin mazaunan kasar da baki da suke yiwo kaura daga kasashen Asiya zuwa kasahen Afrika. Dalilin wannan kaurar kuwa ance juyin mulkin da ya faru tsakanin Banu Abbas da Banu Umayya a Bagadaza, shi ya sanya wasu sukayi kaura suka zauna a Afrika ta Arewa wanda yake daga nan ne suka bazu cikin Afrika ta yamma musamman ta fuskar kasuwanci. Sai dai kuma an ce yayin da suke wannan kaurace-kaurace ne kamanninsu da harshensu da al’adunsu suka canza saboda auratayya da canjin yanayin rayuwa. Har ila yau an kara da cewa ana zaton mutane sunfi dadewa a Dauara da Kano, ba don komai ba kuwa sai don su ne aka gwada kuma aka ga akwai dadadden tarihinsu da yadda mutane suka yi rayuwa a wadannan wurare.

Madogara: Littafin Asalin Bunkasar Harshen Hausa Na Bashir Ibrahim.
Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button