Asharaf Muhammadu Sanusi Lamido yayi abin kunya
Asharaf Sanusi Lamido yayi abin kunya a idon hausawa..
Dan Gidan Tsohon sarkin kano Asharaf Muhammadu Sanusi na II Yayi abin kunya a mahangar hausawa a Lokacin da BBCHausa Ta Gayyaci asharaf din domin tattanawa ta yana gizo kai tsaye a karshen tattaunawar tasu da wakilin BBC abdulbaki Jari ya tambayi dan gidan sarki da cewa shin a karshe wacce Shawara zaka bawa matasa? sai kuwa malam asharaf ya buda baki yace afwan menene matasa? Sai shi Abdulbaki ya ce Ana nufin Youths ma’ana dai ya fada masa da kalmar turanci a Lokacin sai ya gane ma’anar matasa,
wannan batu yaja hankali matasa ya kuma jawo cece kuce Tsakanin matasan a shafukan sada zuminci na zamani wasu na ganin ba karamin abin kunya bane ace dan gidan tsohon sarki kamar na jihar kano garin hausa tushen hausa kuma ace bema san ma’anar matasa ba
kuna ganin haka abin kunyane?