ASIRI YA FARA TONUWA…………
Daga Kais Dauda Sallau
Na dade ina gayawa mutane cewa, wannan World Health Organisation (WHO) ba abinda ta ke kitsawa a duniya sai makirce-makirce da sunan suna taimakawa al’umma. Dasu Amnesty International, kotur duniya da wadansu NGO duk mafi yawansu an kirkire su ne domin cutar da wadansu al’umma.
Duk mai hankali yasan wadannan mutane ba za su taba dauka kudadensu suna kashe muku ba tare da suna da manufofin da su ke son su ci ba. Walau suna sace muku dukiya ta wani hanya kokuma suna da wata manufa na cutar da ku a boye.
Ita ma America tana daya daga cikin masu amfani da wadannan ire-iren kungiyoyi, Allah ne ya fara tona asirin su. Kawai a wannan karon tafiyar America 🇺🇸 da WHO bai zo daya bane shiyasa shugaban kasar America 🇺🇸 ya ke zargin WHO, suma WHO su ke zargin shugaban kasar America 🇺🇸 Donald Trump da yin sakarci gurin dakile Coronavirus.
Ai ba yau aka saba yin irin wannan makircin ba, amma tunda bakin su daya ne lokacin kowa shiru yake yi. Wannan karon da Coronavirus ta yi wa America 🇺🇸 bazata, ai ka ji sun fito sun yi magana.
Allah ya kara tona asirin su, ya karya duk wani mai zalunci.