Labarai

ASSU tace ko wanne dalilin jami’a ya shirya komawa Makaranta a mako Mai Zuwa.

Spread the love

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce wa daliban su shirya komawa Makarantu a mako mai zuwa.

ASUU ta fadi haka ne a shafinta na Tuwita yayin da kungiyar ilimi ta bayyana fatan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Kungiyar kwadagon ta bayyana kwarin gwiwar cewa daliban za su koma jami’o’i a mako mai zuwa bayan ganawarsu da gwamnatin tarayya.

Majiyar ta tweeter ta karanta cewa: “Duk daliban jami’ar tarayya su shirya domin komawa Makarantar saboda muna sa ran kyakkyawan sakamako daga ASUU a ranar Laraba.”
Wannan na zuwa ne bayan da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, a ranar Juma’a, ya bayyana fatan cewa za a kammala yarjejeniya da Kungiyar a mako mai zuwa. Ngige ya koka kan yadda ASUU ba ta la’akari da irin kalubalen da bukatunsu zai haifar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button