Kasashen Ketare

ASUU: Ta Koka Da Yunkurin Ganduje Na Mayar Da Asbitin Jami’ar Wudil Gun Kasuwanci.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Kungiyar Asuu rashen Jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudul dake jihar Kano, sun nuna rashin jin dadin su, na yadda gwamnatin jihar kano ke kokarin mayar da ginin Daula Otel wajan kasuwanci wanda kuma Asbitin Jami”ar ne.

Kamar yadda mun rawaito muku, Shugaban Kungiyar Muhammad Sani Gaya da Sakataranta Murtala Muhamad sune suka bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’ar data gabata, tare da nuna kin amin cewarsu da kudirin gwamnatin jihar Kano.

Idan zaku tuna mun rawaito muku cewa Gwamnatin jihar Kano Na duba shawar-warin data samu na mayar da ginin Daula Otel kuma Asbitin Jami’ar KUST zuwa wajan saye da sayarwa.

Sabuda haka ASUU tayi kira ga gwamna Ganduje ya kara bada himma wajen tallafawa ilimi maimakon sanya dukiyar jama’a ga wani bangare na daban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button