Labarai

Atiku Abubakar Ya Caccaki Matakin NBC Na Dakatar Da Gidajen Talabijin Kan Zagin Shuwagabanni

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa matakin da NBC ta dauka na cewa duk wanda ya zagi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Gwamnoni da sauran masu rike da mukaman gwamnati za’a kulle gidan talabijin dinsa ya yiwa ‘yancin yada labarai karan tsaye.

A jiyane NBC ta fara amfani da sabuwar tararta ta Miliyan 5 akan gidan rediyon Nigeria Info dake Legas. Kaman yanda Aka ruwaito muku cewa NBC ta ci Gidan rediyon tarar kudinne saboda baiwa tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya damar cewa akwai gwamnan Arewa da shine kwamandan Boko Haram.

Hakanan NBC ta fitar da sanarwar cewa za’a dakatar da gidan talabijin din daya bari aka Zagi shuwagabanni.

Anfahinci A martaninsa, Atiku yace ko da kuwa masu laifi a kasashen da suka ci gana ba’a hanasu damar bayyana ra’ayoyinsu akan laifukan da suka aikata a kasashen da suka ci gaba.

Atiku ya kuma bayyana cewa, tabbas kalaman kiyayya na da hadari amma kuma a sani cewa babu kasar data yi nasarar yakar ta’addanci ta hanyar hana kafafen watsa labaranta aiki yanda ya kamata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button