Siyasa

Atiku ba bakon yin rashin nasara a zabe bane, a ko da yaushe yana sha kayi a yunkurinsa na shugabancin kasar nan tun 1993 – Tinubu

Spread the love

Zababben shugaban kasar ya bayyana koke-koken Atiku a matsayin ba kawai na banza bane, har ma da cin zarafin kotu ne.

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a ko da yaushe yana shan kaye a yunkurinsa na shugabancin kasar nan tun 1993.

Tinubu ya roki Atiku da kada ya kalli rashin sa a zaben da ya gabata a matsayin bakon abu, yana mai cewa zai zama abin al’ajabi ga jam’iyyar PDP da dan takararta idan aka yi la’akari da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar kafin zabe da kuma lokacin zabe.

Zababben shugaban kasar ya bayyana haka ne a martanin da ya mayar kan karar da Atiku da PDP suka shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa inda suke rokon kotu ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ko kuma kotu ta bayar da umarnin a sake zaben.

Ya kara da cewa Atiku ba shi da tsayayyen tsarin siyasa, kuma ya yi asarar mafi yawan manyan magoya bayansa, duba da yadda yake tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

Tinubu ya kuma bayyana cewa fitowar Atiku a matsayin dan takarar PDP ne ya kara ruruta wutar rikicin da ke faruwa a jam’iyyar, wanda ya sa gwamnoninta guda biyar suka yanke shawarar yi masa aiki tare da tabbatar da cewa ya sha kaye.

Tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Wole Olanipekun ne suka shigar da martanin zaben shugaban kasa.

Zababben Shugaban kasar ya bayyana karar a matsayin ba kawai ta banza ba har ma da cin zarafin tsarin kotu.

Ya ce tun da farko PDP ta shigar da kara a kotun koli, ta hannun wasu gwamnoninta, inda ta bukaci a soke zaben, ba za ta iya ci gaba da shari’o’i biyu kan batu guda a kotuna daban-daban a lokaci guda ba.

Ya bayyana cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, jam’iyyar PDP ta hannun gwamnoninta na jihohin Adamawa, Akwa-Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Sokoto sun shigar da kara a kotun koli, inda suka bukaci da a soke zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya kuma nuna rashin amincewa da cancantar karar a kan cewa an cire Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) da Rabiu kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) duk da cewa masu shigar da kara sun fafata da sakamakon zaben jihohin da suka samu nasara. LP da NNPP.

Masu shigar da kara sun koka kan sakamakon zaben da aka gudanar a jihohin Abia, Anambra, Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Imo, Kano, Plateau da Lagos, kuma ba a bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben gaba daya ba a jihohin.

Martanin ya bayyana cewa ba za a iya sanya Tinubu ya kare wani zagon kasa da ake zargin an tafka a kowace jihohin da aka ambata a baya ba.

Martanin da tawagar Tinubu ta bayar ya kare ne da tambaya kan koken Atiku kan sakamakon zabe a dukkan jihohin da shi Obi ya lashe zaben da suka hada da Adamawa, Bauchi, Akwa-Ibom, Bayelsa, Gombe, Yobe, Sokoto. Jihohin Osun, Kebbi da Katsina, ba tare da sun mayar da kansu masu amsa wannan bukata ba; yayin da a karkashin sashe na 133 (2) na dokar zabe, 2022, jam’iyyar da ake kalubalantar zabenta za ta zama mai amsa tambayoyi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button