Atiku Ya Shawarci Buhari Da Yayi Aiki Da Hankali Wajen Mgance Zanga-zanga Ba Da Karfi Ba…
Yanzu Ne Lokacin Da Za A Yi Amfani Da Hankali Maimakon Zalinci, Masu Zanga-zangar #EndSARS Ba Marasa Hankali Bane, Suna Da Nufi Mai Kyau, Kuma Sun Aikata Abin Da Ya Dace, In Ji Atiku Abubakar.
Abinda Atiku Abukakar Ya Fadawa Shugaba Muhammad Buhari Wanda Ya Samu Tsokaci 6000 Cikin Mintuna 9…
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya shiga shafukan sada zumunta don mayar da martani game da karuwar tashin hankali tsakanin masu zanga-zangar da gwamnati.
Atiku ya shawarci Buhari da ya yi amfani da hankali maimakon tilastawa masu zanga-zangar saboda yin amfani da karfi zai haifar da karin tashin hankali da fitina daga mutane.
Ya rubu a shafinsa na Twitter kamar haka: Lokacin da gwamnati ta nuna cewa ta damu, ‘yan ƙasa za su yi abu mai kyau. Yanzu ne lokacin da za a yi amfani da hankali, maimakon zalunci. Kuma a kan haka ne, nake kira ga @Buhari da ya yi magana da ‘yan kasa, musamman ma matasa na Najeriya.
Masu zanga-zangar #EndSARS ba marasa hankali ba ne; suna da nufi mai kyau, kuma sun aikata abin da ya dace.
Wannan lokaci ne da za a yi kira zuwa ga dalilansu ta hanzarta aiwatar da buƙatunsu da suka dace. Amfani da iyakar ƙarfi zai tsananta, maimakon magancewa.