Siyasa

Atiku Ya Shawarci Buhari A Twitter

Spread the love

ATIKU ABUBAKAR YA BAWA SHUGABAN KASA BUHARI SHAWARAR SAYAR DA JIRAGEN FADAR SHUGABAN KASA.

Atiku Abubakar ya bayar da shawarar ne sakamakon matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na rage kasafin kudin kasar saboda faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya.
A sanarawa da yafitar ranar Alhamis a shafinsa na Twitter ya bayyana cewa :.
“Kar ka rage albashin ma’aikata, amma ka rage na masu da madafun iko. Sannan ka saida jirage 8 ko 9 a cikin jiragen fadar shugaban kasar”
Sannan yakara sa cewa
“Ya kamata a rage kasafin kudi mai matukar yawa na fadar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya. Dole a soke kasafin kudin da aka yi na saya wa shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa da sauran masu rike da mukaman siyasa motocin alfarma.”

Daga: Abdullahi Ibrahim Manzo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button