Labarai
Atiku Yayi Allah Wadai da Karin Farashin Wutar lantarki da gwamnatin Buhari tayi..
Tsohon mataimakin Shugaban Kasa alh Atiku Abubakar Yayi Allah wadai da Karin farashin kudin wutar lantarki a Nageriya inda yace Bamu amince da karin kudin wutar lantarki ba. A daidai wannan lokacin ‘yan Nijeriya yanzu suna buƙatar ƙarfafawa ne ba wai yin watsi da matsalar da suke fuskanta ba. ‘Yan Najeriya da yawa ba su samu kudin da suke samu ba tsawon watanni ba tare da su aikata laifin komai ba Wannan karin bai dace da wannan lokacin ba kuma ba Abu bane Mai kyau