Labarai

Atiku zai kashewa arewa milyoyin kudi

Spread the love

A cewar tsohon mataimakin shugaban ‘kasa Alh. Atiku Abubakar! ‘Jari ita Ce mafi abinda yake wahalar da matasar mu a Najeriya, Zan kuma yi tafiya dasu ‘Dari bisa ‘Dari a harkoki na’ koda ba a siyasance ba, sannan kuma zan basu tallafi mafi tsoka, don kowa ya Dogara da kansa.

A inda yaci gaba da Cewa’ zan zuba makudan kudade, don farfado da kamfonin da suka mutu a duk fadin Arewacin Najeriya, domin samun Raguwar matasa masu zaman banza da muke dasu a Najeriya, Musamman a nan nahiyar tamu Arewa.

Kana mataimakin Shugaban kasar yace’ ba zaiyi hakanba, har sai yayi zama da masu ruwa da Tsaki a harkokin Kasuwanci a Najeriya, domin gaiyato Gwamnati ta shigo Cikin Wannan al’amarin.

Bayan haka Atiku Abubakar yayi wannan furucinne. A yayin halartan sa wani Babban taro na masu hannun jari a ‘kasashen turai inda taron ta gudana a ‘kasar dubai, bayan kammala wannan taron inda manema labarai sukayi masa dafifi, don jin abinda zaice’ duba ga yanda shikadai ne aka samu ‘Dan Najeriya Wanda halarta wannan taron, a dai-dai irin Wannan Lokacin ne Atiku yake baiyama manema labarai irin Shirin sa na Alheri a nan gaba ga Matasar Najeriya.

Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button